Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta kama wani mutum mai suna Abubakar Sanusi bisa zargin hannu a satar ƙarafunan digar jirgi.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, SP Nafiu Habib, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa.
Sanarwar ta ce jami’an ’yan sanda sun samu bayanan sirri game da satar ƙarafunan digar jirgin a ranar 17 ga Agustan 2026, inda suka bi sawun kayan zuwa wani gida da ke unguwar Doya.
Rundunar ta ce jami’anta sun samu nasarar ƙwato ƙarafunan digar jirgin tare da kama Abubakar Sanusi, wanda ake zargi da hannu a satar.
A halin yanzu, ’yan sanda na ci gaba da gudanar da bincike domin gano tare da kama sauran mutanen da ake zargin suna da hannu a aikata laifin.
Rundunar ta tabbatar da cewa za ta ɗauki matakin da ya dace kan duk wanda bincike ya tabbatar da hannu a lamarin.