Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta sanar da dakatar da duk wata hulɗar kasuwanci da hada-hadar kuɗi da Iran har sai baba-ta-gani, sakamakon ƙara tsananta rikicin da ke faruwa a yankin.

Ma’aikatar Harkokin Wajen UAE ta ce matakin ya biyo bayan ƙara tsananta rikicin da take ganin yana barazana ga zaman lafiya da tsaron yankin da kuma duniya baki ɗaya.

Sa’o’i kaɗan kafin sanarwar, Ma’aikatar Tsaron UAE ta ce ta gano makamai masu linzami kirar ballistic guda biyu da aka harbo daga Iran zuwa cikin ƙasar.

Ma’aikatar ta ce ɗaya daga cikin makaman ya faɗi ne a wajen ruwan UAE, yayin da ɗayan ya faɗa cikin ruwanta.

Tun bayan fara hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran, UAE na daga cikin ƙasashen yankin da suka fuskanci hare-haren Iran.

Sai dai tun bayan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Washington da Tehran, hare-haren da ake kai wa UAE sun tsaya, har zuwa lokacin da sabon rikicin ya sake ƙara tsananta.

Matakin na UAE na dakatar da hulɗar kasuwanci da kuɗi da Iran na iya ƙara matsin lamba na tattalin arziki da diflomasiyya a yankin, musamman yayin da ake ƙoƙarin rage tasirin rikicin da ya shafi ƙasashen Gabas ta Tsakiya.