Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi watsi da iƙirarin Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) cewa sama da malamai 200 sun ajiye aikinsu a Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) saboda rashin kyawawan yanayin aiki.

Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kaduna, Ahmed Maiyaki, ya shaida wa BBC cewa rahotannin da ASUU ke yaɗawa ba su yi daidai da gaskiya ba.

Maiyaki ya ce gwamnatin jihar ta yi iya bakin ƙoƙarinta wajen biyan da dama daga cikin buƙatun malaman jami’ar cikin sama da shekaru uku da ta yi tana mulki.

A cewarsa, adadin malaman da suka bar jami’ar cikin shekaru ukun bai wuce mutum 50 ba, kuma mafi yawansu sun bar jami’ar ne saboda sauyin wurin aiki, ba wai sakamakon rashin jin daɗin yanayin aiki ba.

Kwamishinan ya ƙara da cewa gwamnatin jihar na ci gaba da tattaunawa da malaman jami’ar domin lalubo mafita kan matsalolin da suka taso.

Ita ma Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) ta musanta iƙirarin ASUU, tana mai cewa ba ta da wani bayani da ke nuna cewa malamai sama da 200 sun yi murabus.

Shugaban jami’ar, Farfesa Abdullahi Ibrahim Musa, ya ce iƙirarin da ASUU ta yi bai yi daidai da bayanan jami’ar ba.

A wata sanarwa da ya fitar, shugaban jami’ar ya ƙalubalanci ASUU da ta gabatar da hujjoji da suka haɗa da sunayen malaman da ake cewa sun yi murabus, ranakun da suka yi murabus da kuma dalilan da suka sa suka bar jami’ar.

Rikicin dai ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen ASUU-KASU kan yanayin aiki da kuma aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Gwamnatin Tarayya da ASUU.