Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ce da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi amfani da cikakken ƙarfin gwamnatin tarayya wajen ganin jam’iyyar APC ta lashe zaɓen gwamnan Jihar Osun, da ya je jihar da kansa domin taimakawa wajen kayar da Gwamna Ademola Adeleke.

Wike ya ce sakamakon zaɓen ya nuna cewa gwamnatin tarayya ba ta yi amfani da tasirinta wajen ƙwace zaɓen domin tabbatar da nasarar APC ba.

Ya bayyana cewa da Tinubu ya yi niyyar ganin APC ta lashe zaɓen ko ta halin ƙaƙa, da shi ma ya je Osun domin shiga cikin yakin neman nasarar jam’iyyar, kuma hakan da ya yi tasiri a sakamakon zaɓen.

Ministan ya bayyana hakan ne ranar Talata bayan ya kammala duba wasu wuraren da ambaliyar ruwa ta shafa a Maitama, Abuja.

Wike ya kuma yi nuni da cewa da abubuwa sun tafi yadda ya kamata, da ya kamata Gwamna Ademola Adeleke ya kasance cikin jam’iyyar APC.

A zaɓen da aka gudanar ranar 15 ga Agustan 2026, INEC ta bayyana Adeleke, wanda ya tsaya takara ƙarƙashin jam’iyyar Accord, a matsayin wanda ya yi nasara, bayan ya lashe ƙananan hukumomi 19 daga cikin 30.

Ɗan takarar APC, Bola Oyebamiji, ya samu nasara a ƙananan hukumomi 11.

Sakamakon zaɓen ya kasance wani gagarumin koma-baya ga APC a jihar, duk da cewa jam’iyyar na kan mulki a matakin tarayya.