An naɗa tsohon kyaftin ɗin Arsenal da tawagar Faransa, Patrick Vieira, a matsayin sabon babban kocin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta maza ta Senegal, Teranga Lions. Wannan ne karon farko da Vieira zai jagoranci tawagar ƙasa a matsayinsa na koci.

Vieira, mai shekaru 50, ya maye gurbin Pape Thiaw, wanda Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Senegal ta sallama bayan da ƙasar ta fice daga gasar Kofin Duniya ta 2026 a zagayen ’yan 16.

An haifi Vieira a Dakar, babban birnin Senegal, kafin iyalinsa su koma Faransa yana ɗan shekara takwas. Daga baya ya wakilci Faransa sau 107, inda ya lashe Kofin Duniya na 1998 da kuma gasar Euro 2000. A matakin ƙungiyoyi kuma ya yi fice sosai musamman a Arsenal, inda ya lashe kofunan Premier League uku.

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Senegal ta bayyana naɗin Vieira a matsayin wani zaɓi na dabarun wasanni da ya yi daidai da burin ƙasar na gina ingantaccen tsarin ƙwallon ƙafa.

Ana sa ran Vieira zai fara aikinsa a lokacin hutun wasannin ƙasashe na watan Satumba, lokacin da Senegal za ta fara shirye-shiryen neman gurbin shiga gasar AFCON 2027.

Kafin wannan naɗi, Vieira ya horar da ƙungiyoyi irin su New York City FC, Nice, Crystal Palace, Strasbourg da Genoa. Ya bar Genoa a watan Nuwamban 2025, kuma tun daga lokacin bai riƙe wata ƙungiya ba.

A Crystal Palace, ya jagoranci ƙungiyar zuwa matsayi na 12 a Premier League a kakar 2021/22, tare da kai wa wasan kusa da na ƙarshe na FA Cup. Najeriya...