Kotun Cape Town a Afirka ta Kudu ta dage yanke hukunci kan shari’ar Chidinma Adetshina, ‘yar asalin Najeriya kuma tsohuwar sarauniyar kyau, zuwa ranar 27 ga Fabrairu 2027.
Shari’ar ta shafi ƙalubalen da Adetshina ke yi kan matakin hukumomin Afirka ta Kudu na tsare ta da kuma yunƙurin fitar da ita daga ƙasar.
A watan Yuni ne hukumomi suka kama Chidinma bayan ta sake shiga Afirka ta Kudu ta kan iyakar ƙasar da Mozambique.
Batun ya samo asali ne daga takaddamar da ta kunno kai kan matsayin ƙasarta da kuma halaccin takardun da take amfani da su wajen zama a Afirka ta Kudu.
An haifi Chidinma a Afirka ta Kudu. Mahaifiyarta ‘yar ƙasar Afirka ta Kudu ce, yayin da mahaifinta ɗan Najeriya ne.
Sunanta ya shiga fagen daga ne a shekarar 2024, bayan da ta kai matakin ƙarshe na gasar zaɓen sarauniyar kyau ta Afirka ta Kudu. Sai dai batun asalinta ya haifar da cece-kuce, lamarin da daga bisani ya kai ga janye ta daga gasar.
Lauyanta na ƙalubalantar tsare ta da kuma shirin hukumomi na fitar da ita daga Afirka ta Kudu, yayin da Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta ƙasar ke cewa ba ta da ingantattun takardun da za su ba ta damar ci gaba da zama a ƙasar.
Yanzu haka ana sa ran kotun za ta sake duba batun tare da yanke hukunci a ranar 27 ga Fabrairu 2027.