Laberiya ta zama ɗaya daga cikin ƙasashen Afirka da suka amince su karɓi baƙin da gwamnatin Amurka ta kora daga ƙasar, inda ake sa ran wasu daga cikin mutanen za su isa Monrovia gobe, Alhamis.

Gwamnatin Laberiya ta ce ta amince da karɓar baƙi har 1,200 a ƙarƙashin shirin gwamnatin Amurka na tura wasu daga cikin mutanen da take kora zuwa ƙasashe na uku.

A watan Satumban shekarar da ta gabata ne gwamnatin Laberiya ta amince da karɓar wasu baƙi na tsawon shekara guda bisa dalilan jin ƙai. Mutanen sun haɗa da waɗanda suka fito daga ƙasashen Afirka da kuma wasu ƙasashen yankin Amurka ta Arewa da ta Kudu.

Ma’aikatar Yaɗa Labarai ta Laberiya ta ce ba za a bai wa ƙasar wani kuɗi ko lada kai tsaye ba saboda karɓar baƙin. Sai dai Amurka za ta taimaka wajen ganin an samu nasarar shirin tare da ƙarfafa tsarin kula da shige da fice na ƙasar.

Gwamnatin Laberiya ta kuma ce baƙin za su samu damar neman mafaka a ƙasar idan suna buƙata. Haka kuma, za su iya ci gaba da zama a Laberiya idan suka zaɓi yin hakan.

Aƙalla ƙasashen Afirka 10 ne aka ruwaito cewa sun amince da wasu yarjejeniyoyi da Amurka domin karɓar mutanen da aka kora daga ƙasar, a ƙarƙashin manufofin gwamnatin Shugaba Donald Trump na tura wasu baƙi zuwa ƙasashe na uku.

Sai dai ba a cika samun cikakken bayani kan yarjejeniyoyin da Amurka ta kulla da ƙasashen ba. Wasu ƙasashe kuma sun samu kuɗaɗe a matsayin wani ɓangare na yarjejeniyoyin. Misali, Eswatini ta karɓi sama da dala miliyan biyar kan karɓar irin waɗannan baƙi.

Matakin Laberiya na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara kan manufofin gwamnatin Amurka na korar baƙi da kuma tura wasu daga cikinsu zuwa ƙasashen da ba ƙasashensu na asali ba.