Gwamnatin Tarayya tace ta kashe Naira tiriliyan 9.39 wajen karin mafi karancin albashi da sauran alawus-alawus ga ma'aikatan gwamnati tsakanin Yuni
2023 da Disamba 2025.
Ministan Kudi, Taiwo Oyedele, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai kan sakamakon gyare-gyaren tattalin arzikin Najeriya da aka yada a gidan talabijin na Channels.
Oyedele ya ce a cikin watanni 31, gwamnati ta samu karin albarkatun kudi na Naira tiriliyan 20.4 daga kudaden da aka samu bayan cire tallafin man fetur, karin kudaden shiga na cikin gida da kuma karin bashi.
Sai dai ya ce ba a bar kudaden ba tare
da yin amfani dasu ba, domin karin nauyin da ya rataya kan gwamnati ya tilasta mata kashe kudaden wajen biyan bukatu daban-daban.
Ya bayyana cewa Naira tiriliyan 9.39, wanda shi ne kaso mafi girma na karin kudaden da aka kashe, an ware shi ne wajen karin albashi, karin mafi karancin albashi da sauran alawus-alawus na ma'aikatan gwamnati.
Oyedele ya kuma bayyana cewa
Gwamnatin Tarayya ta kashe karin Naira tiriliyan 9.37 wajen biyan basussukan waje, musamman sakamakon faduwar darajar Naira, wanda ya kara kudin da ake bukata wajen biyan basussukan da aka karba da dala.