Babban Bankin Ghana ya ƙaddamar da Majalisar Ba da Shawara kan Harkokin Banki da Hada-hadar Kuɗi ba tare da Riba ba (NIFAC), domin taimakawa wajen tsara, bunƙasa da kuma sanya ido kan harkokin banki da sauran ayyukan kuɗi marasa riba a ƙasar.

A wani saƙo da bankin ya wallafa a shafinsa na X, ya bayyana cewa majalisar za ta riƙa ba wa Babban Bankin Ghana shawarwari kan yadda za a tafiyar da, kula da kuma sanya ido kan bankuna da cibiyoyin kuɗi da ke aiki bisa tsarin da ba ya amfani da riba.

A yayin ƙaddamar da majalisar a wannan mako, Gwamnan Babban Bankin Ghana, Dr. Johnson Asiama, ya jaddada muhimmancin samar da ingantaccen tsarin gudanarwa, kare haƙƙin masu amfani da tsarin, da kuma tabbatar da amincewa da kwanciyar hankali a harkokin kuɗi marasa riba.

Sanannen malamin addinin Musulunci ɗan Najeriya, Farfesa Bashir Aliyu, ne zai jagoranci majalisar.

Sheikh Bashir Farfesa ne a Jami’ar Bayero da ke Kano, sannan shi ne shugaban Majalisar Ƙoli ta Harkokin Shari’a a Najeriya (SCSN).

Sauran mambobin majalisar sun haɗa da Dr. Yussuf Adany Al-Badani, Dr. George Baah-Danquah, Adishetu Hamidu Naabo, da Samuel Gameli Gadzo.