Maryam Danazimi Ibrahim, wata ƴar takara daga Najeriya, ta lashe kyautar Riyal 300,000 na Saudiyya, wadda ta kai kusan Naira miliyan 120, bayan da ta zo ta farko a rukunin mata na haddar Alƙur’ani juz’i 60 tare da Tafsiri, a gasar King Abdulaziz International Qur’an Competition ta duniya karo na 46.

Maryam, wadda ta fito daga Jihar Gombe da ke Arewacin Najeriya, ta yi nasara a rukuni na biyu na gasar, wanda ya ƙunshi haddar Alƙur’ani gaba ɗaya, karatu mai kyau, bin ƙa’idojin Tajweed, da kuma Tafsiri.

Maryam na daga cikin ƴan takara 50, maza 25 da mata 25, waɗanda aka bayyana a matsayin waɗanda suka yi nasara a rukuni biyar na gasar.

Waɗanda suka yi nasara a rukuni na biyu:

  1. Maryam Danazimi Ibrahim — Najeriya — SAR 300,000
  2. Amat Al-Rahman Badi Mutahhar Kulaib — Bahrain — SAR 275,000
  3. Amani bint Shaya bin Awad Al-Husaiki Al-Harthi — Saudiyya — SAR 250,000
  4. Zainab bint Ibrahim bin Abdulsalam Idris — Saudiyya — SAR 235,000
  5. Shumoukh bint Faiz bin Hamdan Al-Zanbaqi — Saudiyya — SAR 220,000

Ƙasar Saudiyya ta karrama waɗanda suka yi nasara a King Abdulaziz International Qur’an Competition karo na 46, wadda aka gudanar domin haddar Alƙur’ani Mai Tsarki, karatunsa da Tafsirinsa.

Jimillar kuɗaɗen kyaututtukan gasar ta kai Riyal miliyan 10.26.