Gwamnatin Tarayya ta bayar da gargadin kwanaki bakwai kan yiwuwar fuskantar babban haɗarin ambaliyar ruwa a jihohi 33 na Najeriya, daga ranar 19 zuwa 25 ga Agusta 2026.

Gwamnatin ta ce ana sa ran matakan ruwan koguna za su ci gaba da tashi, lamarin da ka iya haddasa ambaliyar ruwa a wurare daban-daban cikin wannan lokaci.

Jihohin da aka bayyana suna cikin haɗarin ambaliyar sun haɗa da Kaduna, Neja, Taraba, Ondo, Oyo, Rivers, Abia, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bayelsa, Benue, Borno da Cross River.

Sauran su ne Delta, Ebonyi, Edo, Enugu, Gombe, Imo, Jigawa, Kogi, Kwara, Nasarawa, Lagos, Ogun, Osun da Plateau.

Hukumar Kula da Ruwa ta Najeriya (NIHSA) ta yi kira ga al'ummomin da ke zaune a filayen da ambaliya ke iya shafa da su gaggauta komawa wuraren da suke sama domin kare rayukansu da dukiyoyinsu.

Hukumar ta kuma bukaci gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi da su kunna tsarin bayar da gargadin farko tare da fara aiwatar da tsare-tsaren gaggawa domin rage illar ambaliyar.