Dan takarar shugabancin Najeriya na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi alkawarin cewa zai mayar da tallafin man fetur idan ya samu nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Atiku ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da kafafen yaɗa labarai a ranar Laraba, inda ya ce cire tallafin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta yi bai haifar da isasshen amfani ga ’yan Najeriya ba.

Ya ce ya kamata a yi amfani da kuɗaɗen da aka samu sakamakon cire tallafin wajen rage talauci, inganta ilimi da magance matsalolin rashin zuwa makaranta.

Da aka tambaye shi ko zai mayar da tallafin man fetur idan ya zama shugaban ƙasa, Atiku ya amsa da cewa: “Zan mayar, kuma duk wanda ya saci kuɗin zai dawo da su.”

Shugaba Bola Tinubu ya sanar da kawo ƙarshen tallafin man fetur ne a jawabinsa na farko bayan rantsar da shi a ranar 29 ga Mayun 2023, matakin da ya haifar da tashin farashin man fetur da kuma ƙarin tsadar rayuwa a faɗin ƙasar.

Sai dai gwamnatin ta sha nanata cewa cire tallafin na daga cikin matakan da ake ɗauka domin rage nauyin kashe kuɗaɗen gwamnati da kuma sake fasalin tattalin arzikin ƙasa.

A lokacin yaƙin neman zaɓen 2023, Atiku Abubakar ya kuma yi alkawarin sayar da wasu matatun man fetur na ƙasar a matsayin wani ɓangare na shirin gyara harkokin man fetur da tattalin arzikin Najeriya.