Gwamnatin Najeriya ta amince da shirin daina hukunta mutanen da suka yi yunƙurin kashe kansu, a wani mataki da ake ganin zai kawo sauyi a fannin kula da lafiyar ƙwaƙwalwa a ƙasar.
A halin yanzu, mutumin da aka kama da yunƙurin kashe kansa na iya fuskantar hukuncin ɗauri na tsawon shekara guda.
Da yake magana a wata ganawa da manema labarai, Ministan Lafiya na Najeriya, Farfesa Ali Pate, ya ce yunƙurin kashe kai babbar matsala ce a Najeriya, inda ake samun kimanin mutane 300,000 da ke yunƙurin kashe kansu a duk shekara, yayin da kusan 7,000 ke rasa rayukansu sakamakon hakan.
Farfesa Ali Pate ya ce maimakon hukunta mutanen da suka yi yunƙurin kashe kansu, gwamnati za ta mayar da hankali wajen ba su kulawar lafiya, tausayi da kuma taimakon da ya dace.
Mutanen da ke yunƙurin kashe kansu na fuskantar tsangwama a Najeriya, baya ga ƙarancin ƙwararrun ma’aikatan da ke kula da lafiyar ƙwaƙwalwa.
Ƙungiyar Likitocin Lafiyar Ƙwaƙwalwa ta Najeriya ta ce a ƙasar akwai ƙasa da likitan lafiyar ƙwaƙwalwa guda ɗaya ga mutane sama da 200 da ke buƙatar kulawa.