Wani kwale-kwale ya kife a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya, lamarin da ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 40, yayin da ake ci gaba da aikin ceto da neman waɗanda suka ɓace.
Wani jami’in Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ruwa ta Najeriya, Abubakar Yusuf, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce zuwa yanzu an gano gawarwakin kimanin mutane 40.
Lamarin ya faru ne a safiyar jiya Laraba, lokacin da mutane ke kan hanyarsu ta zuwa gonaki a yankin ƙaramar hukumar Goronyo, kamar yadda wani basaraken yankin mai suna Sarkin Daji ya bayyana.
Wani mazaunin yankin, Nasiru Gurau, ya ce masunta ne suka gano tare da fitar da wasu daga cikin gawarwakin, yayin da ake ci gaba da bincike domin gano sauran waɗanda suka mutu ko suka ɓace.
Najeriya na ci gaba da fuskantar yawaitar haɗurran kifewar kwale-kwale, musamman a yankunan karkara, inda ake amfani da su wajen sufuri a wasu lokuta ba tare da isassun matakan tsaro ba.