Majalisar dokokin Bangladesh ta zaɓi Mirza Fakhrul Islam Alamgir a matsayin sabon shugaban ƙasar, a wani zaɓen shugaban ƙasa na farko da aka fafata a kai cikin shekaru 35.

Mista Alamgir, wanda ke cikin jam’iyyar mai mulki ta Bangladesh Nationalist Party (BNP), ya kasance ɗaya daga cikin fitattun ‘yan adawar tsohuwar Firaminista Sheikh Hasina, wadda aka hambarar da ita a shekarar 2024 bayan zanga-zangar ɗalibai da ta rikide zuwa rikicin siyasa.

Alamgir ya taka muhimmiyar rawa wajen jagorantar jam’iyyar BNP a cikin shekaru masu cike da ƙalubale, kuma hukumomi sun taɓa kama shi sau da dama.

Zaɓensa ya zo ne a daidai lokacin da Tarique Rahman ke cika watanni shida a matsayin Firaministan Bangladesh.

A tsarin mulkin Bangladesh, shugaban ƙasa ba shi da manyan ikon zartarwa, domin mafi yawan iko yana hannun firaminista. Sai dai a ƙarƙashin sauye-sauyen kundin tsarin mulkin da ake shirin yi, ana iya ƙara wa ofishin shugaban ƙasar wasu ƙarin iko domin samar da daidaito tsakanin manyan shugabannin ƙasar.