Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC, Dr. Musa Aliyu, a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Dr. Musa Aliyu ya isa fadar shugaban ƙasar da misalin ƙarfe 5:40 na yamma domin ganawar, sai dai ba a bayyana ajandar tattaunawar ba.
Ganawar ta zo ne kwana guda bayan Shugaba Tinubu ya umarci ICPC da ta gudanar da cikakken bincike kan badakalar wata ƙungiya mai suna Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC), wadda ake zargin ba ta da sahihiyar hujjar kasancewarta a matsayin hukuma.
A ranar 6 ga Agusta, Dr. Musa Aliyu ya gabatar wa Shugaba Tinubu da rahoton wucin gadi kan binciken da hukumar ta gudanar. ICPC ta gano cewa PFIPC ba hukuma ce da aka kafa bisa doka ko kuma bisa wani sahihin umarnin gwamnati ba.
Hukumar ta kuma ce mutumin da ke ikirarin kafa PFIPC, Adeniyi Matthew Adeyemi, ya yi amfani da takardun bogi wajen gudanar da ayyukansa, tare da ƙirƙirar wasu hukumomi na bogi.