Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da shirin takaita shigowar manyan motoci cikin birnin Kano daga ƙarfe 6:00 na safe zuwa dare, domin rage cunkoson ababen hawa da inganta zirga-zirga.

Kwamishinan Sufuri na jihar, Haruna Isa Dederi, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai, inda ya ce an kammala shirye-shiryen fara aiwatar da sabuwar dokar.

Dederi ya ce matakin ya zama dole ne saboda ƙaruwa da yawan jama’a a jihar, da kuma matsayin Kano a matsayin babbar cibiyar kasuwanci a yankin.

Ya bayyana cewa shirin wani ɓangare ne na haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar da wani kamfani mai zaman kansa domin zamanantar da tsarin kula da zirga-zirgar ababen hawa da inganta harkokin sufuri.

A cewar kwamishinan, hanyoyin shiga birnin guda shida ne za su kasance ƙarƙashin sabon tsarin. Hanyoyin su ne Kano-Katsina, Kano-Zariya, Kano-Dambatta, Kano-Gwarzo, Kano-Wudil da Hadejia.

Ya ce takaita shigowar manyan motocin zai taimaka wajen rage cunkoso a manyan hanyoyin shiga birnin, tare da sauƙaƙa zirga-zirgar jama’a da harkokin kasuwanci.

Shi ma Manajan Daraktan kamfanin da ke haɗin gwiwa da gwamnatin jihar, Kafilu Abdulkadir, ya ce irin wannan tsarin da aka fara amfani da shi a Jihar Legas a shekarar 2007 ya taimaka wajen rage cunkoson ababen hawa, musamman ta hanyar samar da wuraren ajiye manyan motoci.

Abdulkadir ya bayyana cewa za a gina babbar tashar ajiye manyan motoci a Daka Tsalle, yana mai cewa sama da manyan motoci 3,000 ne ke shiga Kano a kullum.

Ya ce tashar na daga cikin matakan da ake ɗauka domin rage cunkoson ababen hawa a manyan hanyoyin shiga birnin Kano.