Kimanin mutane 48 ne suka rasa rayukansu, yayin da ake ci gaba da neman wasu yara 12 da suka ɓace bayan wani kwale-kwale ya kife a yankin Goronyo da ke jihar Sokoto.

Mafi yawan waɗanda hatsarin ya rutsa da su yara ne, waɗanda suke kan hanyarsu ta zuwa gonaki a safiyar jiya Alhamis.

Da yake magana da BBC, ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Gada da Goronyo a Majalisar Wakilan Najeriya, Bashir Gorau, ya ce masu ninkaya na ci gaba da aikin ceto domin gano sauran yaran da suka ɓace, tare da fatan za a same su da ransu.

Gorau ya ce: “Mafi yawan waɗanda abin ya rutsa da su yara ne da mata, ciki har da yara ‘yan ƙasa da shekara 10.”

Ya ƙara da cewa: “Rafi ya raba mutanen ƙauyen da gonakinsu, shi ya sa a kullum suke amfani da kwale-kwalen katako wajen zuwa gonaki.”

A Najeriya, ana yawan samun haɗurran kwale-kwale da ke haddasa asarar rayuka, musamman a yankunan karkara.

Hatsurran sun fi yawa a lokacin damina, lokacin da rafuka ke cika da ruwa, yayin da ake kuma fama da ƙarancin matakan tsaro, rashin ingancin kwale-kwale da kuma rashin amfani da kayan kariya wajen gudanar da irin wannan sufuri.