Ethel Caterham, wadda ake yi wa kallon mace mafi tsufa da ke raye a duniya, ta cika shekara 117 a yau Juma’a.

Dattijuwar ta yi bikin zagayowar ranar haihuwarta tare da ‘yan uwa da abokan arziki a gidan kula da tsofaffi na Hallmark Lakeview, da ke Surrey a Birtaniya.

An haifi Ethel shekaru uku kafin hatsarin jirgin ruwa na Titanic, sannan shekaru takwas kafin juyin juya halin Rasha. Ta kuma rayu ta ga yakin duniya na farko da na biyu.

A cewar Guinness World Records, Ethel na cikin mutanen da suka fi tsufa da suka tsallake annobar COVID-19, bayan ta kamu da cutar a shekarar 2020 tana da shekara 110.

Ethel ita ce ta ƙarshe a cikin ‘ya’yan iyalinsu guda tara. Ta ci gaba da tuƙa mota har zuwa lokacin da ta kai shekara 97.

A watan Satumban bara, ta karɓi bakuncin Sarki Charles, jim kaɗan bayan bikin cikarta shekara 116. A yayin ziyarar, ta tuna wa Sarki Charles lokacin da aka naɗa shi Yariman Wales a shekarar 1969, lokacin yana da shekara 21.

Ta ce: “Kowace budurwa a lokacin tana son ka, kowa na son ya aure ka.”

Sai dai har yanzu wata Bafaranshiya mai suna Jeanne Calment ce ke riƙe da tarihin mutum mafi tsufa da ya taɓa rayuwa. Ta rasu a shekarar 1997 tana da shekara 122 da kwanaki 164, a cewar Guinness World Records.