Wani sabon rahoto daga ƙungiyar Save the Children ya ce aƙalla yara 180 ne suka rasa iyayensu biyu ko kuma waɗanda ke kula da su sakamakon barkewar cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo.

Rahoton ya ce adadin ya kai kusan yara biyu da ke rasa iyayensu ko masu kula da su a kowace rana tun bayan da aka ayyana barkewar cutar a ranar 15 ga watan Mayun 2026.

Hukumomin lardin Ituri, wanda shi ne cibiyar barkewar cutar, sun ce yara 180 da suka rasa iyayensu sun ƙunshi yara maza 90 da mata 90. Yawancinsu yanzu suna hannun ‘yan uwa ko kuma cibiyoyin kula da yara na gwamnati.

Haka kuma, wasu yara 114 sun rabu da iyayensu yayin da suke karɓar maganin Ebola, inda ƙungiyoyin agaji da ‘yan uwa ke kula da su a halin yanzu.

Save the Children ta yi gargadin cewa yaran da suka rasa iyayensu ko suka rabu da su na fuskantar haɗarin cin zarafi, fataucin mutane, lalata da su, tilasta musu shiga ƙungiyoyin ƴan bindiga, da kuma matsananciyar damuwa ta ƙwaƙwalwa.

Ƙungiyar ta ce tana samar da wuraren kariya da tallafin tunani ga yara a Ituri, inda sama da yara 4,000 ke samun irin wannan tallafi.

A halin yanzu, bayanan Ma’aikatar Lafiya sun nuna cewa sama da 4,945 mutane sun kamu da cutar Ebola, yayin da adadin waɗanda suka mutu ya kai 2,325.