Rundunar Sojin Saman Amurka ta tabbatar da mutuwar mutane takwas bayan wani jirgin sama da ke aiki a ƙarƙashin rundunar ya yi hatsari a jihar Alaska.
Jirgin, wanda wani kamfanin farar hula ke aiki da shi ƙarƙashin kwantiragin gwamnati, ya faɗi da rana a kusa da Cape Newenham, a yankin Anchorage.
Hukumomi sun ce har yanzu ba a bayyana sunayen mutanen da ke cikin jirgin ko kuma takamaiman manufar tafiyarsu ba.
Shugaban Rundunar Sojin Saman Amurka a Alaska, Laftanar Janar Robert Davis, ya bayyana waɗanda suka mutu a matsayin ƙwararru masu sadaukar da kai da ke gudanar da wani muhimmin aiki a cikin yanayi mai matuƙar wahala.
Davis ya ce wannan babban rashi ne mai raɗaɗi ga iyalan sojojin da kuma al’ummomin da rundunar ke yi wa hidima.
Ya ƙara da cewa babban abin da rundunar ta fi mayar da hankali a kai yanzu shi ne tallafa wa iyalan waɗanda suka mutu da abokan aikinsu a wannan lokaci na jimami.
A cewar Rundunar Sojin Saman Amurka a Alaska, jirgin ya taso ne daga babban filin jirgin sama na Anchorage zuwa Cape Newenham, wanda ke da nisan kusan kilomita 725 daga Anchorage.
Masu aikin ceto da suka isa wurin da hatsarin ya faru sun tabbatar da cewa babu wanda ya tsira.
An fara gudanar da bincike domin gano musabbabin hatsarin, yayin da hukumomi suka ce za a bayyana sunayen waɗanda suka mutu ne bayan an sanar da iyalansu.