Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya ce lokaci ya yi da za a kawo ƙarshen yaƙin da ƙasar ke yi da Amurka, yana mai cewa a halin yanzu Iran ce ke da rinjaye.

Pezeshkian ya ce ya fi dacewa a kawo ƙarshen yaƙin yanzu, lokacin da Iran ke da tasiri da mutuncinta, yana mai cewa duniya ta amince cewa ƙasar ta yi nasara.

Ya kuma zargi Amurka da karya dokokin ƙasa da ƙasa ta hanyar kai hare-hare kan makarantu, asibitoci da sauran kayayyakin more rayuwa, yana mai cewa hakan ya sa duniya ta ƙi Amurka.

Shugaban Iran ya soki wasu mutanen da yake cewa ba su fahimci ainihin halin da ake ciki ba, musamman game da matsalolin da gwamnati, kwamandojin sojoji da majalisar dokokin ƙasar ke fuskanta.

Sai dai Pezeshkian ya jaddada cewa kiran da yake yi na kawo ƙarshen yaƙin ba yana nufin Iran za ta miƙa wuya ba.

Ya ce: “Ba za mu miƙa wuya ba ta kowace fuska. Babu tantama a kan hakan. Za mu tunkare su har lokacin da numfashinmu zai fita, kuma za mu azabtar da su.”

Kalaman na shugaban Iran sun zo ne yayin da gwamnatin Amurka ke sauya salon matsin da take yi wa Tehran, inda a yanzu take ƙara mayar da hankali kan matakan matsin tattalin arziki.