An mayar da tsohon Firaministan Pakistan, Imran Khan, gidan yari bayan an kai shi asibiti a Islamabad domin duba lafiyarsa.
Khan, mai shekara 73, an kai shi asibitin gwamnati na PIMS inda likitoci suka duba lafiyarsa kuma suka bayyana shi a matsayin wanda ke cikin ƙoshin lafiya. Daga bisani aka mayar da shi gidan yarin Adiala da ke Rawalpindi da sanyin safiyar Juma’a.
Sai dai jam’iyyarsa ta Pakistan Tehreek-e-Insaf (PTI) ta zargi hukumomi da karya umarnin Kotun Ƙoli, wadda ta bayar da umarnin a kai Khan asibitin Shifa International mai zaman kansa domin samun cikakken kulawar likitoci, ciki har da likitansa na kansa.
Gwamnati ta ce an sauya wurin duba lafiyar ne saboda dalilan tsaro, musamman yadda magoya bayan Khan suka taru a wajen asibitin mai zaman kansa.
PTI ta ce tana shirin shigar da ƙara kan abin da ta kira raini ko karya umarnin kotu, tana mai cewa an mayar da tsohon Firaministan cikin gidan yari bayan 'yan sa'o'i kaɗan da kai shi asibiti.
Tun watan Agustan 2023 ake tsare da Imran Khan a gidan yari sakamakon wasu shari’o’i da hukuncin kotu, yayin da shi da jam’iyyarsa ke ikirarin cewa ana amfani da shari’o’in ne domin murƙushe adawar siyasa.