Tsohon Gwamnan Kano kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC a zaɓen 2027, Rabiu Kwankwaso, ya jajanta wa iyalan mutanen da suka rasa rayukansu a hatsarin kwale-kwale da ya afku a Gorau, ƙaramar hukumar Goronyo ta Jihar Sokoto.

Kwankwaso ya bayyana hatsarin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama a matsayin babban abin takaici, yana mai kira ga hukumomi da su gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin faruwar lamarin.

A cewar rundunar ‘yan sandan Jihar Sokoto, mutane 77 ne ke cikin kwale-kwalen da ya kife yayin da yake ɗauke da manoma da sauran fasinjoji zuwa gonakinsu.

Ya zuwa yanzu, an gano gawarwaki 46, yayin da aka ceto mutane 15 da ransu. Ana kuma ci gaba da neman wasu 16 da ake kyautata zaton sun ɓace.

Kwankwaso ya yaba wa jami’an tsaro, masu aikin ceto da masu ruwa na yankin bisa ƙoƙarin da suke yi wajen ceto waɗanda suka tsira da kuma gano mutanen da suka ɓace.

Ya kuma buƙaci hukumomi da su ɗauki matakan tsaro na musamman a hanyoyin ruwa, domin rage haɗarin faruwar irin wannan mummunan hatsari a nan gaba.