Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya (EFCC) ta janye karar da ta shigar kan Maryam Isah Shehu da Abubakar Shuraim Abdulhamad, waɗanda aka gurfanar a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja bisa zargin aikata laifukan yanar gizo da kuma yaɗa bayanan da hukumar ta ce suna da illa ga mutuncinta.
An gurfanar da mutanen biyu ne ranar Alhamis, 20 ga watan Agustan 2026, a gaban Mai Shari’a Joyce Abdulmalik, kan tuhume-tuhumen da suka shafi cin zarafi da bibiyar mutum ta kafafen intanet, wato cyberstalking.
A cikin wata sanarwa da Shugaban Sashen Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na EFCC, Dele Oyewale, ya fitar ranar Juma’a, hukumar ta ce abubuwan da ake zargin matasan biyu da aikatawa sun saba wa Sashe na 24(2)(c) na Dokar Laifukan Yanar Gizo ta 2015, wadda aka yi wa kwaskwarima a shekarar 2024.
Sai dai Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya yanke shawarar sassauta musu, tare da janye karar, bayan la’akari da roƙon afuwa da mahaifin Maryam Shehu ya gabatar, da kuma kiraye-kirayen wasu ’yan Najeriya masu kishin ƙasa na ganin an janye tuhumar.
Dele Oyewale ya ce Olukoyede ya bayar da umarnin janye tuhume-tuhumen da ake yi wa matasan biyu.
Duk da haka, EFCC ta gargadi jama’a cewa ba za ta lamunci cin zarafi ko ɓata sunan hukumar ta kowace kafar sadarwa ko dandali ba.
Hukumar ta ce Olukoyede ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa EFCC za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta bisa hurumin da doka ta ba ta, tare da sanya muradun ƙasa a gaba.
Janye karar na nufin Maryam Shehu da Abubakar Abdulhamad ba za su sake fuskantar shari’a kan tuhume-tuhumen da suka kai ga gurfanar da su a gaban kotu ba.
EFCC ta kuma buƙaci ’yan Najeriya da su ci gaba da mu’amala da hukumar cikin mutunci da sanin ya kamata, tana mai jaddada aniyarta ta sauke nauyin da doka ta ɗora mata domin moriyar ƙasa.