Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Tunji Disu, ya gargadi ’yan siyasa da su guji ɗaukar matasa ko ba su makamai domin amfani da su wajen kai wa abokan hamayya hari gabanin zaɓen 2027.
Disu ya yi wannan gargaɗin ne ranar Alhamis a Abuja, yayin taron tattaunawa kan shugabancin matasa da tsaron ƙasa, wanda Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta shirya domin bikin Ranar Matasa ta Duniya ta 2026.
IGP ya ce rundunar ba za ta lamunci tashin hankali, mallaka ko amfani da makamai wajen harkokin zaɓe, tsoratar da masu kaɗa ƙuri’a ko lalata dukiyoyi ba.
Ya buƙaci shugabannin siyasa da su guji ɗaukar matasa, ba su makamai ko ɗaukar nauyin tashin hankali, yana mai cewa irin wannan mataki na iya jefa makomar ƙasar cikin haɗari.
Disu ya kuma yi gargaɗi kan ƙara yaɗuwar tashin hankalin siyasa a kafafen sada zumunta, ciki har da yaɗa labaran ƙarya, kalaman ƙiyayya, cin zarafi ta yanar gizo, yin kwaikwayon mutane, deepfake da sauran hare-haren dijital.
Ya shawarci matasa da su tabbatar da sahihancin bayanan da suke samu a intanet kafin su yaɗa su, tare da guje wa duk wani abu da ka iya haddasa rikici ko tashin hankali.
Gargaɗin na IGP na zuwa ne bayan rahotannin kashe-kashe da hare-hare da suka biyo bayan zaɓen Gwamnan Jihar Osun na baya-bayan nan, inda jam’iyyun Accord da APC suka rasa wasu daga cikin mambobinsu.
Daga cikin waɗanda aka kashe akwai Dele Ayegbo, ɗan uwan Wole Oke, Daraktan-janar na yaƙin neman zaɓen APC a jihar, wanda rahotanni suka ce an harbe shi kwanaki biyu kafin zaɓen.
Sai dai Rundunar ’Yan Sandan ta dage kan cewa wasu daga cikin rikice-rikice da kashe-kashen da suka faru gabanin zaɓen suna da alaƙa da ƙungiyoyin asiri, ba wai rikicin siyasa kai tsaye ba.