Sanata Saliu Mustapha, mai wakiltar mazabar Kwara ta Tsakiya, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC, yayin da rikicin cikin gida na jam’iyyar ke ƙara tsananta gabanin zaɓen 2027.
Mustapha ya bayyana cewa ya yanke shawarar ficewa ne bayan tuntubar masu ruwa da tsaki, magoya baya da kuma al’ummar mazabarsa.
Ya ce ya fice ne saboda ganin cewa tafarkin jam’iyyar ba ya ƙara dacewa da manufofinsa da burin mutanen da yake wakilta.
Sanatan ya gode wa shugabannin APC, musamman Shugaba Bola Ahmed Tinubu, bisa damar da ya samu a lokacin da yake cikin jam’iyyar, yana mai cewa ficewarsa ba zai rage jajircewarsa wajen yi wa al’ummar Kwara hidima ba.
Ficewar Mustapha na zuwa ne bayan rikicin cikin gida a APC a Jihar Kwara, musamman kan zaɓen fidda gwani na ɗan takarar gwamnan jihar na 2027, wanda ya samar da Kakakin Majalisar Dokokin jihar, Yakubu Danladi Salihu, a matsayin ɗan takarar jam’iyyar.
Mustapha na cikin waɗanda suka nemi tikitin takarar, kuma daga bisani ya shiga ƙungiyar masu adawa da sakamakon zaɓen fidda gwani, wadda aka fi sani da G15.
Ana danganta rikicin da rashin jituwa kan tsarin da ya samar da ɗan takarar APC, da kuma yadda za a tafiyar da shugabancin jam’iyyar bayan wa’adin Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq.