Gwamnatin Tarayya ta ayyana Talata, 25 ga Agusta, 2026, a matsayin ranar hutun ƙasa domin bikin Maulidin Annabi Muhammad (SAW).
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hakan a madadin gwamnatin tarayya, cikin wata sanarwa da Babbar Sakatariyar Ma’aikatar, Dr Magdalene Ajani, ta fitar ranar Juma’a.
Tunji-Ojo ya taya al’ummar Musulmi a Najeriya da mazauna ƙasashen waje murnar wannan rana, tare da kira ga ’yan ƙasa da su yi tunani kan darussan tausayi, tawali’u da hidima ga al’umma da ke cikin koyarwar da rayuwar Annabi Muhammad (SAW).
Ministan ya ce bikin Maulidi wata dama ce ga al’umma ta yin tunani kan waɗannan kyawawan ɗabi’u da yadda za a yi amfani da su wajen gina ƙasa mai cike da zaman lafiya da haɗin kai.
Ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su yi amfani da wannan lokaci wajen yin addu’ar samun zaman lafiya da haɗin kan ƙasa, yana mai jaddada cewa kare haɗin kan Najeriya nauyi ne da ya rataya a wuyan kowa.
Tunji-Ojo ya buƙaci jama’a da su gudanar da bukukuwan cikin natsuwa da mutunta juna, tare da yi wa al’ummar Musulmi fatan Maulidi mai cike da farin ciki da zaman lafiya.
Ya ƙara tabbatar da aniyar gwamnatin tarayya na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da tabbatar da dorewar zaman lafiya a faɗin ƙasar.