Sama da mutum 100 ne ake zargin an sace bayan wasu hare-haren da ’yan bindiga suka kai wasu kauyuka da dama a ƙaramar hukumar Borgu ta jihar Neja, kamar yadda ’yan sanda da mazauna yankin suka shaida wa BBC.
Rahotanni sun ce maharan, waɗanda ke sanye da kayan da suka yi kama da na sojoji, sun kai hare-haren ne bayan sallar Juma’a, inda suka afkawa kauyukan Dekara, Gidan Zana, Sabon Gida da Masaka.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar Neja, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar hare-haren, yana mai cewa an kashe mutane sama da 40.
Ya ce jami’an tsaro na zargin cewa maharan ’yan bindiga ne da ke cikin ƙungiyoyin masu aikata laifuka, waɗanda suka mayar da garkuwa da mutane da kuma wawure dukiyoyi domin neman kudin fansa sana’a a wasu sassan Najeriya.
Mazauna yankin sun ce ’yan bindigar sun shiga kauyen Dekara bayan sallar Juma’a, inda suka tattara mutane tare da tafi da su cikin dazuzzukan da ke kusa, kafin daga bisani su wuce zuwa wasu kauyukan makwabta.
Wani ɗan majalisar yankin, Jafar Muhammad Shetiman Borgu, ya tabbatar wa BBC cewa an kai hare-haren.
Hare-haren sun faru ne a daidai lokacin da ake samun ƙarin ayyukan ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai a yankin Borgu, wanda ke da iyaka da jihohin Kebbi da Kwara, da kuma Jamhuriyar Benin.
Sabbin hare-haren sun zo ne bayan wasu hare-haren garkuwa da mutane da aka kai a yankin a baya.
A farkon watan Agusta, ’yan sanda sun ce sun ceto mutum 145 bayan da aka sace su daga kauyukan Borgu Konkoso, Kasuwan-Daji, Tungan-Makeri da Shafachi.
Hukumomi sun ce jimillar mutane 308 aka ceto a wani gagarumin samamen tsaro, ciki har da sama da mutane 160 da aka sace a jihar Kwara da ke makwabtaka da Neja.