Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bukaci masu ruwa da tsaki da ke goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu da su mayar da hankali wajen tabbatar da nasarar shugaban a mazabu, ƙananan hukumomi da jihohinsu a zaɓen 2027.
Wike ya ce “duk siyasa a gida take”, yana mai cewa abin da ya fi muhimmanci ba neman mukami a kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa ba ne, illa tabbatar da cewa ɗan takarar ya samu kuri’u a yankunan da suke da tasiri.
Ya bayyana cewa ba ya da niyyar neman matsayin Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC, inda ya ce zai fi mayar da hankali kan jiharsa ta Rivers da kuma Abuja.
Ministan ya kuma jaddada cewa har yanzu ba ya cikin jam’iyyar APC, duk da goyon bayan da yake bai wa Shugaba Tinubu.
Wike ya ce ƙungiyoyin siyasar da suka haɗa kai wajen tallafa wa Tinubu a zaɓen 2023 na iya sake yin aiki tare a 2027, sai dai ya ce tsarin kawancen na iya bambanta daga jiha zuwa jiha.
A cewarsa, abin da ya fi muhimmanci shi ne yadda za a tabbatar da nasarar Tinubu a wuraren da kowanne daga cikin masu goyon bayansa ke da tasiri.
Da yake magana kan ayyukan raya ababen more rayuwa da gwamnatin Tinubu ke gudanarwa a Abuja, Wike ya bayyana su a matsayin wani nau'in “kamfen ta hanyar aiki”, yana mai cewa abin da ya kamata jama'a su duba shi ne ayyukan da gwamnati ta aiwatar, ba wai alkawuran kamfe kawai ba.
Yayin da yake duba ayyukan Apo-Karshi Road da hanyar Bwari-Kubwa mai tsawon kilomita 14, Wike ya ce ana sa ran kammala wasu manyan ayyukan more rayuwa kafin zaɓen 2027.
Ya ce kammala ayyukan zai taimaka wajen inganta zirga-zirga, bunƙasa tattalin arziki da sauƙaƙa harkokin yau da kullum ga mazauna Abuja da yankunan da ke kewaye da babban birnin tarayya.