Iran ta ba da izini ga wasu tankokin dakon man Iraqi da su ratsa mashigar Hormuz, bayan da gwamnatin Baghdad ta yi ta neman wannan dama ta hanyoyi daban-daban, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Iran, IRNA, ya ruwaito.

Rahoton ya ce buƙatar ba da damar wucewar tankokin Iraqi na daga cikin muhimman batutuwan da hukumomin Baghdad suka gabatar yayin ziyarar Kakakin Majalisar Dokokin Iran, Mohammad Baqer Qalibaf, zuwa Iraqi.

Shugaban Iraqi, Nizar Amedi, ya kuma ce Iran ta taimaka wajen ba da damar wasu jiragen ruwa dauke da man Iraqi su ratsa mashigar a cikin 'yan kwanakin nan.

Matakin na zuwa ne a yayin da zirga-zirgar jiragen ruwa ta mashigar Hormuz ta ragu sosai sakamakon rikicin Iran da Amurka, lamarin da ya shafi safarar man fetur da iskar gas a duniya. Rahotanni sun ce zirga-zirgar mai ta mashigar ta yi nisa da matakan da aka saba gani kafin rikicin.

Iraqi na kuma ƙoƙarin nemo wasu hanyoyin fitar da man fetur ɗinta, ciki har da amfani da tashoshin Ceyhan a Turkiyya, Baniyas a Syria da Aqaba a Jordan, domin rage dogaro da mashigar Hormuz.