A daidai lokacin da ’yan Najeriya ke fara bibiyar yadda siyasar zaɓen 2027 za ta kasance, rahotanni sun ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fitar da jerin mambobin kwamitin yaƙin neman sake zaɓensa.

A cikin jerin sunayen da aka sanar a ranar Asabar, an naɗa tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari, a matsayin Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar APC. Haka kuma, Shugaba Tinubu ne zai jagoranci kwamitin a matsayin shugaba, yayin da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, za su kasance mataimakan shugabanni. An kuma naɗa Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, a matsayin sakataren kwamitin.

Sai dai wani muhimmin bayani shi ne cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC, ta fitar da jadawalin zaɓen 2027 tun ranar 13 ga Fabrairu, inda ta tsara fara yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na ’yan majalisar tarayya daga ranar 23 ga Satumba, 2026. Don haka, har zuwa wannan rana ta 22 ga Agusta, ba a fara yaƙin neman zaɓen a hukumance ba.

Wannan na nuna cewa APC ta fara gina cikakken tsarin da za ta yi amfani da shi wajen neman wa Shugaba Tinubu wa’adi na biyu, yayin da zaɓen shugaban ƙasa da na majalisar tarayya zai gudana a ranar 20 ga Fabrairu, 2027.