Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Maryam Ibrahim Dan’Azumi, ’yar asalin Jihar Gombe, murnar lashe gasar musabakar Alƙur’ani ta duniya ta King Abdulaziz International Qur’anic Competition, da aka gudanar a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya.

Maryam ta zo ta farko a rukunin mata, bayan da ta doke sauran mahalarta daga ƙasashe 132 na duniya.

A matsayin kyauta, Maryam ta samu Riyal 300,000 na Saudiyya, wanda ya yi daidai da kusan naira miliyan 120.

Shugaba Tinubu ya yaba wa Maryam bisa ƙwarewa da bajintar da ta nuna wajen haddacewa, karatu da fahimtar Alƙur’ani mai girma.

Ya ce nasarar Maryam ba ta ita kaɗai ba ce, illa nasara ce ga Najeriya baki ɗaya, domin ta ɗaga darajar ƙasar a fagen duniya.

Shugaban ya kuma bayyana Maryam da ’yar’uwarta, Hajara Ibrahim Dan’Azumi, a matsayin abin koyi ga matasan Najeriya.

Hajara ita ma ta samu nasara a wata gasar Alƙur’ani ta duniya da aka gudanar a ƙasar Jordan a shekarar 2024, inda ta zo ta farko.

Tinubu ya yaba wa iyayen ’yan matan, malamansu da masu kula da tarbiyyarsu, yana mai cewa samun irin wannan matsayi na ƙwarewa na buƙatar sadaukarwa, jajircewa da kyakkyawar tarbiyya.

A ƙarshe, Shugaba Tinubu ya yi wa Maryam addu’ar Allah Ya ƙara mata ilimi da hikima, tare da ba ta damar ci gaba da samun nasara a karatun Alƙur’ani da sauran abubuwan da za ta gudanar a rayuwarta.