Jihar Imo ta samu gagarumar nasara a fannin kiwon lafiya, bayan da aka kammala tiyatar da aka yi da taimakon na’urar mutum-mutumi a karon farko a Specialist Hospital da ke Umuguma, Owerri.

Tawagar ƙwararrun likitoci ’yan Najeriya da na ƙasashen waje ce ta gudanar da tiyatar, ƙarƙashin jagorancin Farfesa Kingsley Ekwueme, wani ƙwararren likitan tiyatar mutum-mutumi da ke aiki a Birtaniya, kuma ɗan asalin Jihar Imo.

Da yake magana da manema labarai a cibiyar Imo Robotics and Oncology Centre (IROC), inda aka gudanar da aikin, Farfesa Ekwueme ya bayyana tiyatar a matsayin “cikakkiyar nasara.”

Ya ce fasahar tiyatar mutum-mutumi na da matuƙar amfani wajen maganin wasu nau’o’in cutar daji, musamman kansar ƙasan mafitsara, saboda tana bai wa likitoci damar cire ƙwayoyin da ke ɗauke da cutar tare da ƙoƙarin kare muhimman ayyukan jiki.

A cewarsa, hakan na iya taimakawa wajen rage matsalolin da wasu marasa lafiya ke fuskanta bayan tiyata, musamman matsalar riƙe fitsari da kuma rasa ƙarfin jima’i.

Farfesa Ekwueme ya ce nasarar da aka samu wajen amfani da wannan fasaha wajen maganin kansar ƙasan mafitsara na da matuƙar muhimmanci, yana mai cewa bai kamata marasa lafiya su kasance cikin matsalolin rashin iya riƙe fitsari ko rasa ƙarfin jima’i na dogon lokaci bayan tiyata ba.

Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, wanda ya halarci aikin, ya bayyana wannan nasara a matsayin wani babban ci gaba wajen samar da ingantaccen kiwon lafiya mai sauƙin samu ga al’ummar jihar.

Ya ce cibiyar ba za ta kasance wurin kula da marasa lafiya kawai ba, illa kuma za ta taimaka wajen gano cututtuka tun da wuri da kuma kare al’umma daga wasu cututtuka ta hanyar gudanar da binciken lafiyar jama’a akai-akai.

Uzodimma ya bayyana cewa cibiyar tana aiki ne ƙarƙashin tsarin haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu, wato PPP, inda mafi yawan kuɗaɗen gudanar da ita ke fitowa daga ɓangaren masu zaman kansu.

A cewarsa, wannan tsarin zai taimaka wajen tabbatar da dorewar cibiyar da kuma ingantaccen gudanar da ayyukanta, tare da faɗaɗa damar al’ummar jihar da sauran ’yan Najeriya samun ingantaccen kiwon lafiya na musamman.