Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ce gwamnatinsa ta cika manyan alkawuran da ta ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023, yana mai cewa Najeriya na gab da fara cin gajiyar matakan da aka ɗauka domin farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar.

Tinubu ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya fitar, yayin da aka bayyana sunayen mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar na zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Shugaban ya ce matakan da gwamnatinsa ta ɗauka sun sanya Najeriya a kan hanyar samun ci gaba da bunƙasar tattalin arziƙi.

“Babu shakka mun fito daga cikin duhun da muke ciki, kuma yanzu muna dab da girbar amfanin tattalin arzikin da zai amfani dukkan ‘yan Najeriya,” in ji Tinubu.

Ya ce yayin da ake shirin fara yaƙin neman zaɓen shekarar 2027, gwamnatinsa na da nasarori da dama da za ta gabatar wa ‘yan Najeriya domin su ga irin ci gaban da aka samu.

A cewarsa, za su bayyana ayyukan da gwamnatin ta aiwatar domin ƙara wa ‘yan ƙasa fata da ƙarfafa musu gwiwa a sassa daban-daban na Najeriya.

Tinubu ya kuma bayyana kwarin gwiwarsa cewa gwamnatinsa za ta yi nasara kan dukkan masu ƙoƙarin mayar da Najeriya baya.

Ya buƙaci mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓen da aka kafa da su yi aiki tukuru tare da haɗin kai domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a zaɓen shugaban ƙasa da za a gudanar a watan Janairun 2027.