Rikicin da ke tsakanin Iran da Amurka na daga cikin manyan batutuwan da ake sa ran za su mamaye tattaunawar da Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, da Yarima Mai Jiran Gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, za su yi a birnin Paris a yau Litinin.
A yayin ganawar, shugabannin biyu za su tattauna batutuwan da suka shafi tsaro da siyasa, musamman halin da ake ciki tsakanin Iran da Amurka.
Baya ga wannan, Macron da Mohammed bin Salman za su jagoranci taron farko na sabuwar Majalisar Haɗin Gwiwar Dabarun Siyasa da Tattalin Arziƙi tsakanin Faransa da Saudiyya.
Ana kuma sa ran Faransa da Saudiyya za su rattaba hannu kan wasu yarjejeniyoyi a fannoni daban-daban, ciki har da lafiya, sufuri da makamashi.
Taron na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasashen biyu ke ƙara ƙarfafa alaƙar diflomasiyya da haɗin gwiwa a fannonin tattalin arziƙi da dabarun siyasa.