Ƙungiyar masu fafutukar ballewa daga arewacin Mali, wato Azawad Liberation Front (FLA), ta sake sakin wasu sojojin Mali 20 da ta yi garkuwa da su, inda wasu daga cikinsu suka shafe sama da shekaru uku a tsare.
FLA ta ce sakin sojojin ya biyo bayan wata yarjejeniya ta musayar fursunoni, wadda ta ƙunshi sakin wasu fararen hula da hukumomin Mali suka tsare a Bamako, babban birnin ƙasar.
Wani kakakin ƙungiyar ya ce wasu daga cikin sojojin da aka saki suna cikin “mummunan yanayi da ya shafi jikinsu da tunaninsu”, bayan shafe tsawon lokaci a tsare.
Ya ce wasu daga cikinsu sun kwashe kusan shekaru biyar a hannun ƙungiyar.
Sai dai rundunar sojin Mali ta musanta cewa mutanen da aka musanya da sojojin fararen hula ne.
A maimakon haka, wata majiyar tsaro ta ce an saki aƙalla mayakan FLA takwas ne a matsayin wani ɓangare na musayar.
An kama sojojin da aka saki ne a lokuta daban-daban tun bayan sake tsananta rikicin Mali, ciki har da fadan da aka yi a ƙarshen watan Afrilu da kuma hare-haren haɗin gwiwa da FLA da ƙungiyar JNIM, mai alaƙa da Al-Qaeda, suka kai a farkon watan Yuli.
Sakin sojojin na baya-bayan nan na daga cikin jerin musayar fursunonin da aka gudanar a Mali cikin 'yan kwanakin nan.
A ranar 13 ga Agusta, an saki sama da sojojin Mali 80 da aka tsare tun watan Afrilu, yayin da bayan kwana uku aka sake wasu sojoji shida da suka samu raunuka.