Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta ƙaddamar da wani sabon shirin yaƙi ta sama domin fatattakar “’yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka” da ke addabar jihohin Arewa maso Yammacin ƙasar.
A wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na X, ta ce shirin mai suna “Hannun Ƙarfe” zai tallafa wa dakarun da ke gudanar da hare-haren ƙasa wajen maido da zaman lafiya da tsaro a jihohin Zamfara, Katsina, Sokoto, Kebbi da Kaduna.
Rundunar ta ce dakarun na gudanar da ayyukan ne ƙarƙashin Operation Fansan Yamma, inda rundunar sojin sama ke amfani da dabarun yaƙi ta sama tare da haɗa kai da sauran hukumomin tsaro domin daƙile ayyukan ƙungiyoyin miyagu.
NAF ta ce ƙaddamar da shirin na nuna ƙudurin dakarunta na ƙara amfani da ƙarfin yaƙi ta sama wajen tallafa wa ayyukan tsaro da kuma dakile barazanar ’yan ta’adda a yankin.
A wani saƙo na daban, Rundunar Sojin Najeriya ta kuma sanar da wani shiri na musamman domin kawar da mayakan ƙungiyar Lakurawa a jihohin Sokoto da Kebbi.
Wannan na zuwa ne bayan da ƙungiyar IS a yankin Sahel ta yi iƙirarin ɗaukar nauyin wasu hare-hare da aka kai a jihohin Sokoto da Kebbi a watan Mayu.