Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayar da umarnin sake nazarin jerin sunayen kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC na zaɓen shugaban ƙasa na 2027, bayan ce-ce-ku-ce da suka biyo bayan fitar da sunayen mambobin kwamitin.

Wata majiya daga cikin masu ruwa da tsaki na APC da ke cikin kwamitin ta tabbatar wa BBC cewa an umurci shugabannin jam’iyyar da fadar shugaban ƙasa da su sake duba jerin sunayen sakamakon wasu kura-kurai da aka samu.

Majiyar ta ce daga cikin matsalolin akwai sanya sunayen wasu jami’an gwamnati cikin kwamitin, waɗanda ake ganin bai dace su kasance cikin tsarin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar ba.

Wannan mataki ya zo ne sa’o’i kaɗan bayan fadar shugaban ƙasa ta sanar da kwamitin da ya ƙunshi mutum 223, inda aka naɗa tsohon gwamnan Zamfara kuma Sanata, Abdul’aziz Yari, a matsayin Darakta-Janar.

Daga cikin sunayen da suka janyo tambayoyi akwai Betta Edu, tsohuwar Ministar Jinƙai da Rage Talauci, wadda aka dakatar daga mukaminta a shekarar 2024 bayan zargin da ya shafi badakalar kuɗi.

Haka kuma, wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar da ake ganin ya kamata su kasance cikin kwamitin ba su bayyana cikin jerin farko ba, ciki har da wasu gwamnoni da tsoffin gwamnoni.

Daga cikin waɗanda ba su samu wuri a jerin farko ba akwai tsohon Gwamnan Filato, Simon Lalong, wanda ya jagoranci kwamitin yaƙin neman zaɓen APC a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Haka kuma ba a ga sunan Festus Keyamo ba, wanda yana daga cikin masu magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen APC a shekarar 2023.

Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu, wanda ya jagoranci ɓangaren hulɗa da masu ruwa da tsaki a kwamitin yaƙin neman zaɓen 2023, shi ma ba ya cikin jerin sunayen farko.

Sai dai majiyar ta shaida wa BBC cewa, duk da umarnin sake duba jerin sunayen, ba a janye naɗin Sanata Abdul’aziz Yari a matsayin Darakta-Janar ba.

A cewar majiyar, za a sake nazarin jerin sunayen domin yin gyare-gyare tare da fitar da sabon jerin mambobin kwamitin nan gaba.