Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, ya soki jerin sunayen kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC mai mulki, wanda aka kafa domin tallafa wa takarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.
An fitar da jerin sunayen kwamitin ne ranar Asabar, inda aka naɗa tsohon Gwamnan Zamfara, Sanata Abdul’aziz Yari, a matsayin wanda zai jagoranci kwamitin. Sai dai fitar da jerin sunayen ta janyo muhawara da ce-ce-ku-ce a faɗin ƙasar.
A cikin wata sanarwa, Kwankwaso ya ce jerin sunayen na “daga hankalin ’yan Najeriya waɗanda ke cikin mawuyacin hali a sassa daban-daban na ƙasar”.
Ya kuma nuna damuwa kan wasu daga cikin mutanen da aka sanya cikin kwamitin, musamman jami’an manyan hukumomin gwamnati da ya ce ya kamata su kasance masu zaman kansu daga harkokin siyasa.
Kwankwaso ya ambaci Shugaban Hukumar Tara Kuɗaɗen Shiga ta Ƙasa (FIRS), Dr Zacch Adedeji, da Shugaban Ofishin Kasafin Kuɗi na Tarayya, Tanimu Kurfi, a matsayin wasu daga cikin jami’an da aka sanya cikin jerin.
Ya ce shugabancin muhimman hukumomin gwamnati na buƙatar mutane masu zaman kansu, waɗanda ba sa nuna goyon baya ga wani ɓangare na siyasa, kuma al’umma za ta iya amincewa da su.
Kwankwaso ya kuma yi kira ga Sanata Abdul’aziz Yari, wanda ya amince da jagorantar tawagar yaƙin neman zaɓen APC, da ya sake nazarin matakin da ya ɗauka tare da sauya matsayinsa.
“Ina kira ga Sanata Abdul’aziz Yari, wanda ya amince ya jagoranci tawagar yaƙin neman zaɓen, da ya yi nazari sannan ya sauya tunani,” in ji Kwankwaso.