Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya ce sake dawo da tallafin man fetur zai iya mayar da tattalin arzikin Najeriya cikin matsalolin da ta fuskanta a shekarun baya.
A wata sanarwa da ma’aikatar ta wallafa a shafinta na sada zumunta ranar Litinin, ministan ya ce cire tallafin ya bai wa gwamnati ƙarin damar amfani da kuɗaɗen shiga wajen gudanar da muhimman ayyuka, ciki har da ilimi, lafiya, ababen more rayuwa da tsaro.
Ya ce dawo da tallafin zai sake jefa gwamnati cikin matsin lamba wajen tsara kasafin kuɗi, tare da ƙara mata nauyin kashe kuɗaɗe.
Ministan ya ce masu kira da a dawo da tallafin ya kamata su yi la’akari da abubuwan da ƙasar za ta rasa wajen gudanar da wasu shirye-shiryen raya ƙasa.
A cewarsa, tun bayan cire tallafin a watan Yunin 2023, gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi sun samu ƙarin kuɗaɗen shiga da suka kai kusan naira tiriliyan 15.8 zuwa watan Disamban 2025.
Ya ce daga cikin kuɗaɗen, an kashe kusan naira tiriliyan 6.47 wajen manyan ayyukan more rayuwa, yayin da aka ware sama da naira biliyan 400 ga shirye-shiryen tallafawa jama’a.
Ya ƙara da cewa wasu daga cikin shirye-shiryen sun haɗa da NELFUND, asusun saka hannun jari a gidaje da kuma shirye-shiryen bayar da rance ga ‘yan ƙasa da ‘yan kasuwa.
“Shin mu dawo da tallafin man fetur, ko mu ci gaba da tallafawa shirin lamunin karatu ga matasan Najeriya?” in ji ministan.
Ya kuma tambayi masu sukar matakin cire tallafin ko ya kamata a dawo da shi maimakon ci gaba da bai wa jihohi da ƙananan hukumomi ƙarin kuɗaɗen shiga, tare da ci gaba da samun kuɗaɗen gina hanyoyi, layin dogo, samar da wutar lantarki da inganta tsaro.
Mohammed Idris ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su mayar da hankali kan sauye-sauyen tattalin arzikin da zai samar da fa’ida mai ɗorewa a dogon lokaci.
Ya ce babban burin gwamnatin tarayya shi ne gina tattalin arziki mai ƙarfi wanda zai iya samar da ci gaba mai ɗorewa tare da inganta rayuwar ‘yan Najeriya.