An gano gawar wani Dan acaba mai suna Nura Yusuf, Wanda akai zargin ya bata makonni da suka gabata a wani kango bayan ya dauki wasu fasinja zuwa hanyar Gas Pipeline a Unguwar Sabo-Tasha, a kan hanyar Abaji-Gwagwalada da ke Babban Birnin Tarayya Abuja


Rahotanni sun nuna cewa marigayin, ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Bagwai ta Jihar Kano, ya ɗauki wasu fasinjoji da suke nufin yankin Gas Pipeline, inda ake zargin an shake shi.


Wani abokin marigayin na kud da kud, Ibrahim Baba, wanda ya tabbatar wa wakilinmu da lamarin a ranar Litinin, ya ce an gano gawar Dan acabar har ta fara ruɓewa a cikin wani kango da ba a kammala ba a yankin ranar Asabar.


Ya ce wasu manoma da suke kan hanyarsu zuwa gonakinsu ne suka gano gawar bayan sun ji wani mummunan wari yana fitowa daga cikin ginin.


A cewarsa, an bayyana cewa Dan acabar ya ɓace tsawon makonni da dama kafin a gano gawarsa ranar Asabar.


Baba ya ce nan take aka sanar da ‘yan sanda, kuma jami’an tsaro suka gaggauta zuwa wurin da aka gano gawar.