Wani jigo a jam’iyyar ADC, Dino Melaye, ya bukaci Shugaba Bola Tinubu da mukarrabansa da su fara tattara kayansu daga Fadar Shugaban Ƙasa.
Ya na mai bayyana cewa ADC za ta doke jam’iyyar APC mai mulki a babban zaɓen shekarar 2027.
Melaye ya ce sakamakon zaɓen zai Kara fito da rashin gamsuwar ’yan Najeriya da gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, wadda ya zarga da gaza magance matsalolin yunwa, rashin tsaro da sauran ƙalubalen da ke addabar ƙasar.
Dino malaye ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi kafar Arise TV a ranar Litinin.
Malaye ya jaddada kwarin gwiwa kan damar ADC na samun nasara, yana mai cewa dabarar da jam’iyyar za ta bi wajen lashe zaɓen abu ne mai sauƙi, domin ’yan Najeriya a shirye suke su ga sauyin gwamnati.
Yana mai cewa yan Najeriya Sun gaji da rashin cika alkaura, Sun gaji da ciwo bashi, sun gaji da kasafin kuɗi uku a jere da ba a aiwatar da su ba.