Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci ’yan ƙasar da su ƙara dagewa wajen yin addu’o’i domin samun mafita ga matsalolin tsaro da sauran ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta.
Tinubu ya bayyana hakan ne a cikin saƙonsa na ranar Maulidi, wanda mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar.
Shugaban ya buƙaci Musulmai su yi ƙoƙarin yin koyi da koyarwar Annabi Muhammad (SAW), musamman wajen mu’amala da juna da kuma gudanar da rayuwa.
A cewar Tinubu, akwai darussa masu muhimmanci da za a koya daga halayen Annabi Muhammad (SAW), ciki har da dagewa, juriya, haƙuri, tawali’u da rashin nuna son kai.
Ya ce waɗannan kyawawan ɗabi’u za su taimaka wajen ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin ’yan Najeriya.
Haka kuma, shugaban ya yi kira ga malaman addini da su yi amfani da wannan lokaci na Maulidi wajen yi wa Najeriya addu’ar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Ya kuma buƙaci malaman da su yi wa al’umma wa’azi kan muhimmancin koyi da koyarwar Annabi Muhammad (SAW), musamman a harkokin da suka shafi kishin ƙasa da haɗin kan al’umma.
Musulmai a Najeriya da sauran sassan duniya sun gudanar da bukukuwan Maulidin Annabi Muhammad (SAW) a ranar Litinin.
Saƙon na Tinubu ya zo ne a daidai lokacin da Najeriya ke ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro da tattalin arziƙi, yayin da ’yan ƙasa ke kokawa kan tsadar rayuwa da hauhawar farashin man fetur da kayan masarufi.
Matsalolin tattalin arziƙin sun ƙara tsananta tun bayan da Tinubu ya hau mulkin ƙasar a shekarar 2023, musamman sakamakon manyan sauye-sauyen tattalin arziƙin da gwamnatinsa ta aiwatar.