Gwamnatin Indiya ta ce za ta fitar da wani kaso na albasar da ta jibge a rumbunan ajiyarta, domin ƙara yawan kayan a kasuwanni tare da rage tashin farashin da ake fama da shi a ƙasar.
Matakin na zuwa ne yayin da farashin albasa ya yi tashin gwauron zabi, inda matsakaicin farashin sayar da ita a ƙasar ya kai kusan rupee 43.53 kan kowace kilogram a ranar 24 ga Agusta, lamarin da ya nuna ƙarin kusan kashi 59 cikin ɗari idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.
Gwamnatin ta ce farashin albasa kan samu ƙaruwa a watan Agusta da Satumba sakamakon sauye-sauyen yanayi, ƙarin buƙata musamman a lokacin bukukuwa, da matsalolin jigilar kayayyaki.
A wani ɓangare na matakan rage farashin, gwamnatin ta fara amfani da jiragen ƙasa na musamman da ake kira “Kanda Express” wajen jigilar albasa daga Nashik zuwa manyan biranen da farashin ya fi ƙaruwa, ciki har da Delhi, Chennai, Kochi, Madurai da Guwahati.
Haka kuma, gwamnati za ta sayar da albasar da ta fitar daga rumbun ajiyarta kan farashi mai rahusa, inda aka tsara sayar da ita a wasu kasuwannin sayar da kaya kai tsaye kan rupee 35 kan kilogram ɗaya.
A Delhi-NCR kuwa, ana shirin amfani da motoci masu ɗauke da albasa domin rarraba ta ga al'umma a wurare daban-daban, da nufin rage wa masu saye nauyin tashin farashin.
Gwamnatin Indiya ta ce ƙasar na da isasshen albasa da za ta biya buƙatar cikin gida, inda aka kiyasta samar da albasa a shekarar 2025/26 da kusan tan miliyan 30.7.