Fadar shugaban ƙasar Rasha ta ce ba ta da wani bayani kan dalilin da ya sa wani jirgin jigilar kaya na sojojin Amurka ya sauka a filin jirgin Vnukovo da ke birnin Moscow.

Jirgin, wani Boeing C-17 Globemaster III mai lambar rajista ta Amurka 07-7181, ya sauka a Moscow a ranar Talata, bayan ya taso daga Riga, babban birnin Latvia. Bayanai daga manhajar bibiyar zirga-zirgar jiragen sama ta Flightradar24 sun nuna cewa jirgin ya isa Riga ne a ranar 23 ga Agusta, bayan ya taso daga Camp Springs da ke Maryland, inda sansanin sojin sama na Andrews yake.

Har yanzu ba a tabbatar da ko jirgin na ɗauke da fasinjoji ko kayan aiki ba, yayin da Fadar Kremlin ta ce ba ta da wani bayani game da jirgin ko manufar zuwansa Moscow.

Lamarin ya haifar da ce-ce-ku-ce a kafafen yaɗa labarai na Rasha, inda ake hasashen cewa wataƙila jirgin ya shiga ƙasar ne domin wani aikin diflomasiyya, ko kuma wata musayar fursunoni tsakanin Rasha da Amurka.

Wasu kuma sun danganta zuwan jirgin da yiwuwar sabuwar tattaunawa kan yaƙin Ukraine, musamman ganin cewa a baya jiragen Amurka sun kai wakilan musamman na Shugaba Donald Trump, Steve Witkoff da Jared Kushner, Moscow domin tattaunawa da Shugaban Rasha Vladimir Putin.

Sai dai har yanzu babu wata hujja da ta tabbatar da cewa Witkoff ko Kushner na cikin jirgin da ya sauka a Moscow a wannan karon. Reuters ta ce ba a iya tabbatar da waɗanda ke cikin jirgin ko abin da yake ɗauke da shi ba.

Saboda haka, duk wata magana da ke cewa jirgin ya kai jami'an Amurka Moscow domin tattaunawa ko musayar fursunoni tana nan a matsayin hasashe, ba tare da tabbacin hukuma ba.