Uwargidan Shugaban Ƙasar Najeriya, Oluremi Tinubu, ta buƙaci Musulman ƙasar da su yi koyi da rayuwa da koyarwar Annabi Muhammad (S.A.W) yayin da suke bikin Maulidin bana.

A cikin saƙon taya murna da ta fitar domin zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W), Uwargidan Shugaban Ƙasar ta ce bikin na ɗauke da muhimman darussa da suka haɗa da tausayi, yafiya da kuma zaman lafiya tsakanin al’umma.

Ta taya al’ummar Musulmi murna tare da yi musu fatan alheri, inda ta shawarce su da su rungumi kyawawan ɗabi’un da Annabi Muhammad (S.A.W) ya koyar, tare da tabbatar da zaman lafiya a gidajensu, al’ummominsu da ma ƙasar baki ɗaya.

Oluremi Tinubu ta bayyana cewa kyawawan ɗabi’u da halayen Annabi Muhammad (S.A.W) har yanzu suna da matuƙar muhimmanci wajen ƙarfafa haɗin kai da kyautata dangantaka tsakanin ’yan Najeriya.

Ta kuma bayyana fatan cewa bikin Maulidin zai ƙara ƙarfafa zumunci da haɗin kai tsakanin ’yan ƙasa, tare da kawo sabon fata, zaman lafiya da albarka ga Najeriya.

Uwargidan Shugaban Ƙasar ta kuma yi addu’ar samun zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki a Najeriya, yayin da Musulmai ke gudanar da bukukuwan Maulidi.