Rundunar ’Yan Sandan Jihar Nasarawa ta gargadi jam’iyyun siyasa da su guji duk wani mataki da ka iya kawo cikas ga zaman lafiya ko jefa rayukan jama’a da dukiyoyinsu cikin haɗari.
Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Mohammed Jauro Shetima, ne ya bayyana hakan yayin wani taro da shugabannin jam’iyyun siyasa suka gudanar a Lafia, babban birnin jihar.
An gudanar da taron ne a daidai lokacin da harkokin siyasa ke ƙara ɗaukar zafi a jihar, inda aka tattauna muhimmancin gudanar da kamfe, gangami da sauran harkokin siyasa cikin lumana, tare da bin tanadin doka.
CP Shetima ya buƙaci jam’iyyun siyasa da su ja kunnen magoya bayansu kan guje wa taruwa da daddare, musamman a kan manyan tituna, saboda irin waɗannan taruka na iya toshe zirga-zirga, haifar da tashin hankali da kuma samar da damar samun arangama tsakanin magoya bayan jam’iyyun da ke hamayya.
A cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, SP Ramhan Nansel, ya fitar, an ce kwamishinan ya kuma umurci jam’iyyun siyasa da su sanar da rundunar ’yan sanda tun kafin gudanar da duk wani gangami, jerin gwanon siyasa ko babban taron siyasa.
Ya ce hakan zai bai wa rundunar damar ɗaukar matakan tsaro da suka dace domin kare jama’a da kuma hana yiwuwar rikici ko durƙushewar doka da oda.
Kwamishinan ya kuma jaddada buƙatar ’yan siyasa su guji yaɗa kalaman batanci, maganganun ƙiyayya, kalaman tayar da hankali da kuma duk wani mataki da ka iya ƙara tsananta rikicin siyasa.
CP Shetima ya tabbatar wa jam’iyyun siyasar jihar cewa rundunar ’yan sanda za ta kasance tsaka-tsaki, ƙwararriya kuma mai jajircewa wajen samar da yanayin da zai bai wa dukkan jam’iyyun siyasa damar gudanar da ayyukansu cikin adalci da tsaro.
A nasu ɓangaren, shugabannin jam’iyyun siyasar da suka halarci taron sun gode wa kwamishinan bisa shirya taron, tare da yin alƙawarin ƙara ƙoƙari wajen tabbatar da zaman lafiya, bin doka da oda a dukkan harkokin siyasarsu.