Aƙalla mutum 27, ciki har da yara huɗu, ne suka mutu sakamakon sabon rikicin da ya ɓarke a jihar Kordofan ta Kudu da ke Sudan.
Rahotanni sun ce hare-haren sun faru ne a yankunan Qardud da Abu Hamama, inda al’ummar Otoro ke zaune, yayin da wasu mata suka samu raunuka.
Ƙungiyar Likitocin Sudan ta zargi ƙungiyar ’yan tawayen SPLM-N, ƙarƙashin jagorancin Abdel Aziz al-Hilu, da hannu wajen kai hare-haren.
Ƙungiyar ta ce an kai hare-haren ne kan fararen hula a daidai lokacin da rikici tsakanin SPLM-N da al’ummar Otoro ke ƙara tsananta.
A cewar ƙungiyar, hare-haren sun tilasta wa mutane da dama barin gidajensu zuwa yankunan Abu Hitan da Kadugli domin neman mafaka.
Ƙungiyar Likitocin Sudan ta yi gargaɗin cewa ci gaba da kai hare-hare kan fararen hula bisa bambancin ƙabila na iya rikidewa zuwa wani babban rikicin ƙabilanci a yankin.
Ta kuma bayyana hare-haren da aka kai kan mata da yara marasa makami a matsayin abin da ya saɓa wa ƙa’idojin dokokin jinƙai na ƙasa da ƙasa.