Gwamnatin Tarayya ta ce za ta sake duba kwangilolin hanyoyin da aka bai wa kamfanoni a matsayin rangwame, sakamakon matsanancin cunkoso da kuma lalacewar babbar hanyar Benin zuwa Asaba.
Ministan Ayyuka, David Umahi, ya bayyana hakan ne bayan ya gudanar da duba halin da hanyar Benin-Asaba ke ciki, inda ya soki kamfanin BAECC da ke kula da aikin, yana zarginsa da rashin ƙwarewar fasaha wajen gudanar da aikin.
Umahi ya ce kamfanin ya cire kwalta daga wasu sassan hanyar ba tare da fara gina magudanan ruwa ba, lamarin da ya ƙara jefa hanyar cikin mummunan hali. Ya kuma sanar da cewa gwamnati za ta kawo wani ɗan kwangila domin yin aikin gaggawa na gyara hanyar tare da rage wahalar da matafiya ke fuskanta.
Matsalar hanyar ta janyo cunkoso mai tsanani, inda wasu matafiya da direbobi suka kwashe kwanaki suna makale a hanya. Wasu direbobi sun ce tafiyar da ake yi cikin sa'o'i daga Legas zuwa Asaba yanzu na iya ɗaukar kwanaki saboda lalacewar hanyar.
Kamfanin BAECC kuwa ya ce yawan ruwan sama da kuma cunkoson ababen hawa sun kawo cikas ga aikin, musamman wajen gina magudanan ruwa da kuma kammala sassan da aka fara.
Gwamnatin ta kuma ce za ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki domin sake duba yarjejeniyar rangwamen hanyar da kuma tabbatar da cewa sharuddan kwangilar suna aiki yadda ya kamata.